AmanaOnline

Coronavirus ta kama Ministan Lafiya

Coronavirus ta kama Ministan Lafiya
  • An kama Sanata a Kenya kan kalaman kiyayyaDaga Ferdinand Omondi BBC News, NairobiAn kama wani dan majalisar dattawa a Kenya bayan an zarge shi da furta kalaman kiyayya a wata hira ta talbijin.Masu bincike sun jagoranci Ledama Olekina, sanatan yankin Narok zuwa ofishin hukumar hadin kan kasa domin yi masa tambayoyi.Hukumar tana da ikon gurfanar da duk wanda ake zargi da nuna wariya ko tayar da rikici a kan wata kabila ko mabiya wani addini.Masu suka sun ce hukumar ba ta da wani karfi kuma har yanzu ta kasa hana ‘yan siyasa furta kalamai masu cike da takaddama.A hirar ta talbijin, Mr Olekina ya soki wasu al’umomi da ke neman shugabanci a yankin da kabilar Maasai suka fi yawa.Mr Olekina ya kare kalaman nasa inda ya ce yana magana ne a madadin jama’arsa wadanda tsawon shekaru ake take su sannan ‘yan siyasa suke kwace musu filaye.Amma masu caccakarsa sun ba da misali da kundin tsarin mulkin Kenya wanda ya bai wa ‘yan kasar damar zama da aiki da kuma mallakar dukiya a kowane bangare na kasar.Wasu kuma sun ce kalaman nasa na iya haifar da rikicin kabilanci.Article share tools
  • An wallafa a 15:1815:18LABARAI DA DUMI-DUMIOlisa Metuh zai sha daurin shekara bakwai a gidan yariWata babbar kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekara bakwai kan tsohon kakakin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Olisa Metuh.Kotun ta yanke masa hukuncin ne bayan ta same shi da laifin almundahanar N400m.Da yake yanke hukunci a yau, alkalin kotun, Mai shari’a Okon Abang, ya ce ya samu tsohon jami’in na PDP ne da laifin halatta kudin haramun.Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ce ta shigar da shi kara, inda ta zarge shi da karbar kudin daga hannun tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha’anin tsawo, Kanar Sambo Dasuki.Article share tools
  • An wallafa a 15:0215:02Coronavirus ta kama ministan lafiyaKaramin ministan lafiya a Iran ya kamu da cutar Coronavirus yayin da cutar ke ci gaba da bazuwa a kasar.Adadin wadanda suka mutu bayan kamuwa da cutar ya kai mutum 15.Akwai rahotannin da ke cewa adadin wadanda suka mutun ya zarta haka.A birnin Qom na Iran ne cutar ta fara bulla wanda kuma birni ne da mabiya mazhabar Shi’a a fadin duniya ke zuwa ziyara a-kai-a-kai.Haka ma an samu rahotannin bullar Cutar Covid-19 a kasashen Afghanistan da Iraqi da Bahrain.A yanzu ana fargabar bullar cutar a sauran kasashen da ke makwabtaka ganin yadda matafiya ke baluguro a yankin.Getty ImagesCopyright: Getty ImagesAdadin wadanda suka mutu bayan kamuwa da cutar ya kai mutum 15Image caption: Adadin wadanda suka mutu bayan kamuwa da cutar ya kai mutum 15Article share tools
  • An wallafa a 14:2414:24’Yan majalisar dattawan Najeriya na so a kafa sansanin soji a GarkidaMajalisar dattawan Najeriya ta nemi rundunar sojin kasar ta kafa sansanin soji a yankin Garkida da ke jihar Adamawa.Mayakan da ake zargi na kungiyar Boko Haram ne sun sha kai hari a garin na Gakirdam inda ko a makon jiyar sai da suka fatakki mutane daga garin bayan sun kashe wasu daga cikinsu.Amma a zamanta na ranar Talata, majalisar dattawan ta ce kafa sansanin soji a yankin zai kawo karshen yawan hare-haren da ake kai wa a garin.Social embed from twitterThe Nigerian Senate@NGRSenate · 5hReplying to @NGRSenateSenator Aishatu Dahiru cites Orders 42 & 52 and moves a motion on the Insurgent attack on Garkida, a town in Gombi Local Government Area of Adamawa State.The Nigerian Senate@NGRSenateSenate resolves to:
   1. Urge the Chief of Army Staff to establish a military command base in Garkida;311:32 AM – Feb 25, 2020Twitter Ads info and privacySee The Nigerian Senate’s other TweetsRahotoReport this social embed, make a complaintArticle share tools
  • An wallafa a 14:1814:18Ministocin EU sun amince da tsarin Birtaniya na tattaunawar kasuwanciMinistocin Tarayyar Turai sun nuna yardarsu kan tattaunawa da Birtaniya bayan da kasar ta fice daga EU.Daftarin – wanda majalisar kula da harkokin Tarayyar Turai ta amince da shi ranar Talata – zai zama tushen tattaunawar da Michel Barnier zai jagoranta.Ya ce ya kamata ka’idojin EU su zama abin dubawa kan duk wata yarjejeniyar kasuwanci a nan gaba.A hannu guda kuma, ministocin Burtaniya sun amince da matakin da gwamnati ta dauka na tattaunawar, wadda aka fara a ranar Litinin.Za kuma a wallafa yarjejeniyar a intanet sannan a gabatar da ita gaban majalisa ranar Alhamis.EPACopyright: EPAMicheal Barnier zai jagoranci tattaunawa da Birtaniya kan alakar kasuwanci a nan gabaImage caption: Micheal Barnier zai jagoranci tattaunawa da Birtaniya kan alakar kasuwanci a nan gabaArticle share tools
  • An wallafa a 13:4313:43’Za a shawo kan Coronavirus a Iran’Shugaban Iran ya bukaci ‘yan kasar su kwantar da hankalinsu yayin da ake kokarin dakile bazuwar sabuwar cutar numfashi ta Coronavirus.Hassan Rouhani ya bayyana cewa kasar za ta shawo kan cutar wadda ta kashe akalla mutum 16.Iran ta ruwaito mutum 95 da suka kamu da cutar ta Covid-19 tun makon jiya amma ana tunanin adadin ya zarce haka.Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce abin damuwa ne yadda ake samun karuwar cutar.WHO ta ce za ta aike magunguna da sauran kayan gwajin cutar ga Iran waadanda ake sa ran isarsu kasar nan da kwana daya ko biyu.Shugaba Rouhani ya yi kira ga mutane da su kiyaye shawarwarin da ma’aikatar lafiya ta ba da.AFPCopyright: AFPArticle share tools
Tags
Share

0 Comments

No Comments Yet!

There are no comments at the moment, do you want to add one?

Write a comment

Write a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

WP2Social Auto Publish Powered By : XYZScripts.com