AmanaOnline

Sarki Mai Duka – by Dr Aliyu U. Tilde

Sarki Mai Duka – by Dr Aliyu U. Tilde

Sarki Maiduka

Ya rabbi sarki maiduka
Sarkin da ba ya lammuka
Kullum kana kan ayyuka
Shirye ni domin in maka
Wake na baiti bai daya.

Na mika hannaye sama
Guiwa a kas ba gardama
Jaki da kaya ba zama
Na zo ina ma sallama
Na bar mutanen duniya.

Tun fil azal kai wanzuwa
Kullum kana kan rayuwa
Ba ka uba ko dan’uwa
Wallahi ni nai rantsuwa
Kai ne kadai ba kishiya.

Kai ne iyakar kwarjini
Zatin da ba tsoka, jini
Komi na bayi ka sani
Aikinmu duk dai ka gani
Barna muke duk safiya.

An bar ka an bar tabbaci
An kama shirme babu ci
Kuka ake duk lokaci
Mai bin ka ba ya firgici
Sarkin da ba ya murdiya.

In ka yi kyauta ba fad’i
Sannan a gode kai dad’i
Ka ba wa sarki mai nad’i
Bayinka muma ba had’i
Yalwarka sai dai godiya.

Sarkin da bai saurin fushi
Fuskarka kullum murmushi
Kullum ka bayar ba rashi
Kai ba ka kwace ko fashi
Kominka na kan gaskiya.

Mulkinka ya kai ko’ina
Tun fil azal ya bayyana
Kaka da rani damina
Tuddai, duwatsu, koguna
Komi duhu ko walkiya.

Mulkinka ba mai takara
Kai ne guda ba ka tara
Ba a saya ko kakara
Sai dai a zo domin bara
An mika kai ba tirjiya.

Mulkinmu yau sai “tenuwa”
Ko da na dukkan rayuwa
In an gama ba ya yawa
Farkonsa murna gun hawa
Karshe nadama don wuya.

Sanya mu bayi masu bi
In mun gaza ko da rabi
Karbe shi tamkar ratibi
Tara mu tutar Annabi
Ranar wuya ba zilliya.

Karo salatin Sayyidi
Manzonka Mamman Abidi
Dukkan sahabban Rashidi
Har mu mabiyyan Hamidi
Wannan da kab ba gaskiya.

Tammat al-hamdulillah

Dr. Aliyu U. Tilde
3 June 2018

Tags
Share

0 Comments

No Comments Yet!

There are no comments at the moment, do you want to add one?

Write a comment

Write a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

WP2Social Auto Publish Powered By : XYZScripts.com