An Fara Ce-ce-ku-ce A Nijar Kan Barazanar Sojoji Ta Gurfanar Da Bazoum A Kotu
Wannan sabuwar dambarwa ta kunno kai ne kwana guda bayan da wata tawagar manyan malaman addinin Islama daga Najeriya ta kai ziyarar shiga tsakani a rikicin siyasar kasar.
Yayin da makusantan hambararen Shugaban ke cewa zargin ba shi da tushe, ‘yan rajin kare hakkin ‘dan adam na cewa gurfana gaban shara’a ba matsala ba ce to amma mafi kyau a guji ramuwar gayya ko kuma abubuwan da ke kama da bita da kullin siyasa.
A sanarwar da ya karanto a kafar talbijan mallakar gwamnati, Kakakin Majlissar soja ta CNSP Kanar Manjo Amadou Abdourhamane ya yi bayani dangane da yadda Shugaban ya yi zargin sojojin juyin mulki sun hana masa damar samun amfani da wasu mahimman abubuwan more rayuwa da kuma a wani gefen jerin takunkumin da CEDEAO ta kakaba wa Nijar da maganar amfani da karfin bindiga don mayar da shi akan mukaminsa.
Ya kara da cewa gwmnatin Nijar ta tattara dukkan bayanai da hujjoji domin gurfanar da hambararen Shugaban kasa da wasu abokansa na ciki da wajen kasa a gaban kotu sakamakaon zargin su da cin amanar kasa da yunkurin tada hankalin kasa a bisa la’akari da bayanan hirarakinsa da wasu mutane na nan gida da Shugabanin wasu kasashen waje da na kungiyoyin kasa da kasa.
Da yake bayyana ra’ayinsa akan wannan sabuwar dambarwa jigo a kungiyar Sauvons Le Niger Alhaji Salissou Amadou na mai ganin dacewar matakin a bisa wasu dalilai.
To sai dai a na su bangare makusantan Shugaba Mohamed Bazoum irinsu Alhaji Mahamadou Sahanine na jam’iyar PNDS Tarayya na kalobalantar abin, wanda a cewar sa wannan tamkar karin maganar nan ne da ke cewa kura ce ke ce wa kare maye.
A cewar .dan rajin kare hakkin ‘dan adam Dambaji Son Allah bai ga matsala ba akan maganar gurfana gaban koliya, mafi mahimmanci shine a yi shara’a cikin yanayin adalci.
A wani abinda ke da nasaba da juyin mulkin na 26 ga watan Yuli wasu ‘yan kasa sun fara kiraye-kirayen ganin Majalissar CNSP ta cafke tsohon Shugaban kasa Issouhou Mahamadou domin a cewar masu irin wannan tunani kusan dukkan laifukan da ake zargin an tafka a tsawon shekaru 12 na mulkin PNDS ya na da hannu dumu-dumu.
A karshen makon jiya a yayin ziyarar wata tawwagar Malaman Addinin Islama daga Najeriya gwamnatin Nijar ta hanyar Firai Minista Ali Mahaman Lamine Zeine ta jaddada aniyar soma zaman sulhu da bangarorin da ke takaddama a rikicin da ya biyo bayan juyin mulkin da a ka yi a wannan kasa.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma: