Gare ku yan siyasa masu muqami a hannu — by Abdulraheem A Bappa
Gare ku yan siyasa masu muqami a hannu,
Zaben ku akayi ba aikin Gwamnati ku ke ba,
Aikin Jama’a neh kuma duk abunda zai zo hannunku na su neh directly or indirectly,
Kun sa ni Sarai irin halin wahala da al’umma su ke ciki sanadiyan gurbatattun shugabanni musamman na matakin kasa (Nigeria) a sama,
Ku chiro hakkin al’umma da ke hannunku ku ba su abun su, dan Allah mun roke ku,
Ko ba dan siyasa ba, ku tausayawa al’ummar ku, idan lokachi yawuce baya dawowa muna tuanatarku…
Mun zo Lokachin da duk musulmi yake buqatan taimako, nutsuwa da kwanciyan hankali domin samun ikon aiwatar da ibada ga mahichchinmu Allah SWA, (Ramadan),
Ku duba girman Allah ku zo ku taimaki al’umma, abunda zaku bayar yachanja rayuwan mutane na wani karamin lokachi ko qwayar zarra daga abunda ku ke samu bai Kai ba.
Ga zafi, ga matsin rayuwa, ga yunwa sannan ga tunanin mai za’achi yau mai za’a chi gobe, tabbas duk dan siyasa mai riqe da muqami musamman a Arewa idan bai zo ko ba ta zo yataimaka ko ta taimakawa mutane a halin yanzu ba, babu shakka sunan sa ko sunan ta mutumin banza ko mutumiyar banza.
Daga karshe, Ina so nayi amfani da wannan dama wajen kira ga wakilan mu na kasa baki daya, musamman na Jahar Yobe (Asalina) da kuma Jahar Kano (Garin da nake rayuwa) da ku taimaka ku raba kayan masarufi da sauran abubuwan kyautatawa ga al’umma domin shiga watan Ramadan mai albarka cikin nutsuwa.
Kano Central: Sen Rufai Hanga, ka zo dan Allah ka taimaki al’ummar ka.
Yobe South: Sen Ibrahim Bomoi, ka zo dan Allah ka taimaki al’ummar ka.
Nangere/Potiskum: Hon Fatsuma Talba, ki zo dan Allah ki taimaki al’ummar ki.
Fika/Fune: Engr Muhammad Buba Jajere, ka zo dan Allah ka taimaki al’ummar ka.
Gwamnonin mu na Arewa duka lokachi yayi da zaku taimaki al’umma. Haka zalika yanmajalisun Jaha da sauran masu ruwa da tsaki da masu hannu da shuni lokachi yayi da zaku cheto al’umma daga halin matsin rayuwa.
Inayiwa kowa barka da Jumu’ah tare da fatan alkhairi. Bissalaaam.
Abdulraheem Adamu Bappa
Friday, 8th March 2024.