AmanaOnline

News

Police Reform: Mece ce dokar sauya fasalin aikin ƴan sandan Najeriya? (BBC)

Police Reform: Mece ce dokar sauya fasalin aikin ƴan sandan Najeriya? (BBC)
September 20
00:02 2020

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sa hannu kan ƙudurin dokar sauye-sauye ga ayyukan ƴan sanda na 2020 wanda majalisar dokokin ƙasar ta amince da shi.

Yanzu ya zama doka wadda ta tanadi yadda za a inganta ayyukan ƴan sanda ta fuskar samar masu da kuɗaɗe da kayan aiki yadda yakamata da kuma kare hakkin ɗan Adam don inganta tsaro.

Hon Yusuf Adamu Gagdi dan majalisar wakilai ne a Najeriya da tun farko ya gabatarwa majalisa wannan ƙuduri, ya shaida wa BBC cewa dalilai da dama ne suka sa a ƙirƙiri wannan ƙuduri.

Ga bayanansa:

1. An ce an samar da yadda al’umma za ta sa hannu a cikin aikin ƴan sanda ta wurin ba da bayanan da zai kawo tsaro ga mutane. Da yadda al’umma za ta zama cikin duk wata harkar tsaro da ta same ta, kwanaki shugaban ƙasa ya amince da fitar da kudi biliyan 13 don aiwatar da wannan aiki.

2. Na biyu akwai abun da ya shafi al’umma ta yadda a wasu lokutan yan sanda kan kama mutum har ya yi sa’a 48 ko fiye a hannunsu ba a kai shi kotu ba.

Ya kamata ne daga lokacin aka kama mutum to ya yi sa’a 24 kawai a hannun ƴan sanda a gurfanar da shi a kotu. Idan ƴan sanda ba su iya sakinsa a wannan lokaci ba to sai sun samu umarnin kotu don ci gaba da tsare mutum fiye da tsawon hakan.

3. Sauran abubuwa sun haɗa da yanayin aikin ɗan sanda da albashin ɗan sanda. Sau da yawa za ka ga ɗan sanda akan titi amma albashinsa bai fi daga naira 30,000 zuwa naira 45,000 ba a wata.

Ana nufin mutum yana kan titi yana aiki tsawon wata daya amma a biya shi wannan ɗan kuɗi? Bai je ya kula da iyalansa sosai ba, to yaya ma kuɗin za su ishe shi cin abinci, sa sutura da sayen man mota?

4. Wannan doka ta ɗauki ƙudurin gyara hakkin ƴan sanda don ganin an magance maganar karɓe-karɓen kuɗi a hanya.

5. Haka kuma daga ran da aka samar da hukumar ƴan sanda za ka ga shugabanninta wani ya yi shekara ɗaya ne ya tafi, wani kuma biyu sai ya tafi, ba a bari shugabannin su daɗe a kan matsayi don yin gyaran da suka zo yi.

Wannan doka ta gyara hakan cewa ya kamata ofishin shugaban ƴan sanda ya samu kariya ganin wurin ya tsaya tsawon wani lokaci kamar shekara huɗu, don samun damar yin gyaran da ya kamata. Ba wai yai shekara ɗaya kawai ya tafi ba, ka ga an samu matsala.

Idan har aka ga yana daukar shekarau bai aikin

Tags

AmanaOnline Newsletter

We give a quick summary of the latest Breaking news and Topical opinions from Nigeria.

Search AmanaOnline

Disclaimer

Disclaimer


The information contained in this portal is for general information purposes only. The information is provided by AmanaOnline.com.ng.

While we endeavour to keep the information up to date and correct, we make no representations or warranties of any kind, express or implied, about the completeness, accuracy, reliability, suitability, availability or guarantees, with respect to the claim and/or the website, or the information, the products, the services, or the related graphics contained on the website, for any purpose.

Any reliance you place on such information is therefore strictly at your own risk.
Information presented on this website is considered public information (unless otherwise noted) and may be re-distributed or copied.

Use of appropriate byline/photo/image credit is requested.

AmanaOnline © 2001

Archives

Reset password

Enter your email address and we will send you a link to change your password.

Get started with your account

to save your favourite homes and more

Sign up with email

Get started with your account

to save your favourite homes and more

By clicking the «SIGN UP» button you agree to the Terms of Use and Privacy Policy
Powered by Estatik
Enable Notifications OK No thanks