AmanaOnline

News

A Binciki Zargin Sayen Muƙamai da aka yi wa Wasu Ministoci -Kakakin Atiku 

A Binciki Zargin Sayen Muƙamai da aka yi wa Wasu Ministoci -Kakakin Atiku 
October 25
22:12 2026

A binciki zargin sayen muƙamai da aka yi wa wasu ministoci -Kakakin Atiku

Daga Wakilinmu

Kakakin Yaɗa Labaran ɗan takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi kira da a binciki zargin da wani kakakin yaɗa labarai na kamfen ɗin neman sake zaɓen shugaban ƙasa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.

Kakakin na Atiku mai suna Paul Ibe, ya ce ya kamata a gaggauta binciken zargin da Alwan Hassan ya yi wa wasu ministoci, a cikin wata tattaunawa mai zafi da aka yi da shi a gidan talabijin na ARISE TV.

Ibe ya yi wannan kiran gaggawa ne da ya nemi a yi wa bincike mai zaman kansa, a wani rubutu da ya fitar a ranar Juma’a, a shafin sa na Facebook, inda kuma ya haɗa da wallafa bidiyon tattaunawar da ARISE TV ta yi da Hassan.

A cikin tattaunawar wadda wakilinmu shi ma ya saurara, Hassan ya yi zargin cewa wasu ministoci kuɗi suka biya kafin a naɗa su kam muƙamai.

A kan haka ne sai Paul Ibe ya bayyana cewa, “wannan zargi fa ba daga ’yan adawa ne ’yan Nijeriya suka ji an yi wannan zargin ba. Alwan Hassan, mai magana da yawun Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaba Tinubu ne ya yi zargin cewa wasu ministoci sun biya kuɗaɗen da suka kai biliyoyin nairori domin samun naɗin mukamai, daga bisani kuma suka nemi hanyoyin da za su fanshe kuɗaɗensu.

A cikin tattaunawar dai Hassan ya ce wasu ministoci kan biya biliyoyin na’urori domin a naɗa su kan muƙamin minista. Ya ce ba ya na nufin yanzu kaɗai ba, har a can gwamnatocin baya. “Dalili kenan a ƙasar nan bayan kafa sabuwar gwamnati, za a ga ministoci ne ake fara damƙewa.” Inji Alwan Hassan.

Kan haka ne sai Ibe ya ce: “Wannan babban zargi ne da ya fito daga cikin tawagar siyasar Shugaban Ƙasa da kansa. Don haka, abin da ake buƙata shi ne amsoshi, ba sake kai wa ’yan adawa hare-haren zagi ba.”

Daga nan sai Ibe ya yi tambaya cewa: “Waɗanne ministoci ne suka biya kuɗin? Wa ya karɓi kuɗaɗen? Waɗanne hujjoji ne Hassan yake da su? Kuma me Shugaba Tinubu ya sani game da wannan batu?”

Ya ci gaba da cewa tun kafin waɗannan kalamai, an taɓa jin zarge-zargen da ke danganta Femi Gbajabiamila, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, da karɓar kuɗaɗen da suka shafi neman naɗin minista.

Don haka Zarge-zargen da Hassan ya yi sun ƙara nuna muhimmancin gudanar da bincike mai zaman kansa kan tsarin naɗe-naɗen mukaman gwamnati.

“Haɗarin wannan lamari a bayyane yake: idan aka mayar da muƙamin gwamnati wani jari da ake saya, to hidimar jama’a za ta iya rikiɗewa zuwa hanyar neman dawo da kuɗin da aka kashe. A irin wannan yanayi, buƙatun ’yan ƙasa na samun ingantacciyar lafiya, ilimi, wutar lantarki da ayyukan yi za su iya zama saniyar-ware, yayin da masu riƙe da muƙaman gwamnati suka fi mayar da hankali kan dawo da jarin da suka zuba.

“Saboda haka idan zargin Hassan gaskiya ne, ’yan Najeriya suna da haƙƙin sanin ko ma’aikatun gwamnati suna yi wa jama’a hidima ne, ko kuwa suna taimaka wa wasu mutane wajen dawo da kuɗaɗen da suka kashe. Wannan batu yana haifar da tambayoyi masu tayar da hankali game da abubuwan da wannan gwamnati take bai wa fifiko, musamman ganin yadda wasu ke bayyana rashin gamsuwa da ayyukanta.

Rahotanni sun nuna cewa Hassan ya yi waɗannan kalamai ne yayin da yake kare matakan taƙaita kuɗaɗen da ake ware wa ma’aikatun gwamnati. Sai dai hana ma’aikatu kuɗi ba zai maye gurbin binciken zargin cin hanci da rashawa ba.

Bai kamata a hana ’yan Najeriya muhimman ayyukan gwamnati saboda zargin cewa wasu jami’ai sun sayi muƙamansu ba.

“Ina kira ga hukumomin EFCC da ICPC ya kamata su karɓi hujjojin da Hassan yake da su, sannan su binciki duk waɗanda aka ambata, ba tare da la’akari da matsayinsu ko alaƙar siyasarsu ba.”

Sai kuma Ibe ya yi tambaya cewa idan irin waɗannan zarge-zarge sun shafi ’yan adawa, shin hukumomin za su ci gaba da jan-ƙafa haka?

“Ya kamata Shugaba Tinubu ya fito ya yi magana kai-tsaye kan wannan batu. Ba zai dace tawagar yaƙin neman zaɓensa ta nemi ’yan Najeriya su sake ba shi wa’adin mulki ba, alhali mai magana da yawunta yana tayar da tambayoyi game da ko sai an biya kuɗi kafin mutum ya samu shiga majalisar ministocinsa.”

Ya ce ma’aikatun Najeriya amana ce da aka damƙa wa masu riƙe da muƙaman gwamnati domin yi wa jama’a hidima. ’Yan Najeriya sun cancanci ministocin da suka duƙufa wajen yi wa al’umma aiki, ba waɗanda ake zargi da neman dawo da kuɗin da suka kashe wajen samun muƙamai ba.” Cewar Ibe.

AmanaOnline Newsletter

We give a quick summary of the latest Breaking news and Topical opinions from Nigeria.

Search AmanaOnline

Disclaimer

Disclaimer


The information contained in this portal is for general information purposes only. The information is provided by AmanaOnline.com.ng.

While we endeavour to keep the information up to date and correct, we make no representations or warranties of any kind, express or implied, about the completeness, accuracy, reliability, suitability, availability or guarantees, with respect to the claim and/or the website, or the information, the products, the services, or the related graphics contained on the website, for any purpose.

Any reliance you place on such information is therefore strictly at your own risk.
Information presented on this website is considered public information (unless otherwise noted) and may be re-distributed or copied.

Use of appropriate byline/photo/image credit is requested.

AmanaOnline © 2001

Archives

Reset password

Enter your email address and we will send you a link to change your password.

Get started with your account

to save your favourite homes and more

Sign up with email

Get started with your account

to save your favourite homes and more

By clicking the «SIGN UP» button you agree to the Terms of Use and Privacy Policy
Powered by Estatik
Enable Notifications OK No thanks